Zaben 2023: Kotu ta Kori Dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC a jihar Abia.

APC Convention
APC Convention

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana tsohon karamin ministan ma’adinai da karafa, Dakta Uchechukwu Ogah, a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Abia.

Mai shari’a Binta Nyako a hukuncin da ta yanke, ta tabbatar da zaben fidda gwanin da aka gudanar kai tsaye wanda ya samar da Ogah a matsayin dan takarar APC, shine wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta bubiyi yadda ya kasance.

Mai shari’a Nyako ta soke takarar Cif Ikechi Emenike wanda tun a farko INEC ta amince da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben fidda gwanin gwamna ya gudana a ranar 11 ga Maris, 2023.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya rawaito cewa Ogah, a cikin wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CS/95/2022, ya kai karar babban Cif Ikechi Emenike; APC; Sen. Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar na kasa; INEC da Daniel Eke a matsayin wadanda ake tuhuma na 1 zuwa 5.

Ogah, saboda haka, ya nemi kotun da ta umurci jam’iyyar APC da ta mika sunansa ga INEC a matsayin dan takararta na zaben gwamnan Abia a 2023.

Da take yanke hukuncin, alkaliyar kotun ta amince da wanda ya shigar da kara (Ogar) sannan ta umarci jam’iyyar da ta mika sunansa ga INEC a matsayin wanda aka zaba a matsayin dan takarar gwamnan Abia a zaben 2023.

NAN ta rawaito cewa rikicin ya barke a jam’iyyar APC a Abia bayan da jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwanin gwamna a jihar wanda ya samar da Ogah da Emenike a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar.

Sai dai a hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wanda ke tabbatar da hukuncin da wata babbar kotun jihar Abia ta yanke a baya wadda ta bayyana Emenike a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, INEC a watan Oktoba ta buga sunan Emenike a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan a jam’iyyar APC a zaben 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here