Gwamnatin kano ta fitar da Nera Milyan 300 ga daliban kano dake karatu a jami’ar Cyprus.

Ganduje signs
Ganduje signs

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sakin naira miliyan dari uku a matsayin kudin karatu ga daliban jihar da suka dauki nauyin karatun su a jami’ar Near East dake kasar Cyprus.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano, Sanusi Abdullahi Kofar Na’isa ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce ana cigaba da samun tagomashi a kokarin da gwamnatin jihar keyi na ingantawa tareda karfafawa matasa gwiwa ta hanyar samar da ingantaccen ilimi.

A cewar sanarwar, kwamishiniyar ilimi mai zurfi Dr. Mariya Bunkure ta bayyana cewa biyan bashin yana cika alkawarin da Gwamna Ganduje ya yi na daga darajar zamantakewa da tattalin arziki na hadakar matasan jihar ta hanyar samar da ingantaccen ilimi a lokacin da ya dace.

“Kwamishiniyar ta gode wa Gwamna bisa ganin wannan mafarkin ya tabbata”, inda ta kara da cewa “Babbar Godiya ga mai girma Khadimul-Islam, hakika dattako da halayyar kirkin ka bata da na biyu,” in ji sanarwar.

‘’ Daga nan sai ta yi amfani da wannan damar wajen taya daliban da iyayensu murna kan wannan gagarumin al’amari, inda ta jaddada bukatar yin kyakkyawan amfani da ilimin da aka samu domin ci gaban jihar Kano da ma Nijeriya baki daya’’.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here