Kungiyar ‘Yan mazan jiya ta Najeriya ta karrama wani tsohon sojan Najeriya mai shekaru 109, Mista Mele Ture da wasu da suka yi yakin duniya na 1 da na 2 bisa sadaukar da kai ga Al’ummar kasa.
Shugaban kungiyar Manjo-Janar Abdulmalik Jibril ya ce an karrama fitattun mutanen ne saboda irin rawar da suka taka a lokacin yake-yake wanda ya kawo daukaka ga kasar nan.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rawaito cewa taron wanda aka shirya, hadin gwiwa ne da gidauniyar Green Heroes da akai masa taken “Bikin Jaruman mu”.
Ya ce an shirya taron ne domin karrama jaruman sojan kasar da suka yi ritaya, inda ya kara da cewa ana gudanar da taron ne aduk shekara.
A cewarsa, wadannan mutane sun sadaukar da rayuwarsu ne tareda dakatar da sha’awarsu dan cikar burin biyan bukatun kasa da muradun ‘yan kasa.
“Wadanda aka karrama a yau sune tsaffin soji dasukai yakin basasa, tsoffin sojojin ECOMOG dasukai yaƙe-yaƙe a Laberiya da Saliyo, Tsohon Sojan Bakasi da tsoffin sojojin da suka shiga cikin tashin hankali kuma ba su dawo ba.
“Da yawa daga cikinsu sun sadaukar da kan su kuma ba su dawo ba, kuma wasu daga cikinsu sun samu munanan raunuka da ke barazana ga rayuwar su.
“Alhamdu lillah, wasun su na nan ayau. Mun tattaro su ne domin tuna musu cewa ba za a iya mantawa da gudummawar su ga al’umma ba.
Mai magana da yawun kungiyar Maj.-Gen. IBM Haruna, ya ce an kafa kungiyar ne a shekarar 1964 domin kula da bukatar tsofaffin sojoji.
Kamfanin dillacin labaran Najeriya ya rawaito cewa kadan daga cikin wadanda aka karrama sun hada da, Air Marshal Mohammed Umar mai ritaya, AVM Lucky Ararile mai ritaya, Sgt. Ogunde Olasunkanmi, dakuma Sanata Florence Ita-Giwa saboda rawar da ta taka a Bakassi da sauransu.













































