Shugaba kuma mamallakin rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya zargi babban jami’in Hukumar Kula da kayyade farashin Man Fetur NMDPRA Farouk Ahmed, da aikata cin hanci, inda ya bayyana cewa ya kashe Dala Miliyan Biyar wajen biyan kudin karatun sakandare na ’ya’yansa hudu a kasar Switzerland.
Dangote ya yi wannan zargi ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a matatar mai da masana’antar takin zamani ta Dangote da ke Lekki a jihar Lagos.
Inda ya bayyana cewa irin wannan kashe-kashe bai dace da kudin shigar ma’aikacin gwamnati ba, kuma yana barazana ga amincewar jama’a da hukumomin da ke da alhakin sa ido.
Ya bayyana cewa kudin da ake magana a kai ya shafi shekaru shida na karatun sakandare ga yara hudu, inda ya nuna cewa ba za a iya bayyana irin wannan kudin daga albashin aikin gwamnati kadai ba, tare da jaddada cewa masu biyan haraji na da hakkin ganin ana amfani da kudinsu yadda ya dace.
Dangote ya ce wannan lamari yana sanya manyan tambayoyi game da bayyana kadarori, rikicin anfani, da amincin tsarin kula da harkokin man fetur a bangaren kasa, yana mai cewa ya dace a fito a yi wa ’yan Najeriya cikakken bayani kan yadda aka samu kudin da aka kashe.
Ya bukaci hukumomin da suka dace, ciki har da Hukumar Kula da Ka’idojin Halayyar Ma’aikatan Gwamnati ko duk wata hukuma da gwamnati ta ga dama, su gudanar da cikakken bincike domin tantance ko kudin shigar shugaban hukumar ya dace da irin wannan kashe-kashe, yana mai cewa ba dole ba ne a sallame shi kai tsaye kafin a kammala binciken.
Dangote ya kuma kwatanta wannan zargi da halin da talakawan ’yan Najeriya ke ciki, inda da dama ke fama da wahalar biyan kananan kudaden makaranta.
Dangote ya yi gargadin cewa idan aka musanta zargin, zai dauki matakan shari’a domin tilasta bayyana gaskiyar kudaden da aka biya.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Farouk Ahmed bai mayar da martani kan zargin ba.













































