Gwamnatin jihar Kwara ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Rundunar Sojin Najeriya ta kama ‘yan bindiga dauke da makamai a karamar hukumar Ifelodun ta jihar, inda ta bayyana wadannan rahotanni a matsayin karya da yaudara.
Ƙarin bayanin ya biyo bayan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda wasu mutane da aka ce an kama su a Ifelodun suka bayyana cewa an ba su makamai da abin hawa daga bangaren gwamnatin jihar.
Kwamishiniyar sadarwa ta jihar Kwara, Bola Olukoju, ta bayyana cewa babu wani dan bindiga da Rundunar Sojin Najeriya ko wata hukumar tsaro ta kama a karamar hukumar Ifelodun ko a wani bangare na jihar Kwara baki daya.
Gwamnatin ta bayyana cewa bayan duba bidiyon da ke yawo, mutanen da ke ciki sun yi ikirarin mallakar wani abin hawa da suka ce daga gwamnatin Ilorin ne, tare da makamai da suka ce sun samo daga Abuja, amma ba a kama su a cikin jihar Kwara ba.
Karanta: Tinubu ya bai wa jami’an tsaro umurnin mamaye dukkanin dazukan jihohin Kwara, Neja da Kebbi
Ta kuma bayyana cewa an kama mutanen ne a Auchi da ke jihar Edo, kuma babu wata hukuma ta tsaro da ta ruwaito kama ‘yan bindiga a Kwara, yayin da ake jiran karin bayani domin samun cikakken haske kan lamarin.
Gwamnatin jihar Kwara ta jaddada cewa babu wata gwamnati ta jiha da ke da ikon bai wa mutane bindigogin AK-47, tare da bayyana cewa karamar hukumar Ifelodun ta tabbatar da cewa motar tsaro da aka ambata a bidiyon an tanade ta ne domin ‘yan sa-kai masu taimaka wa tsaro, amma daga bisani ba a dawo da motar ba bayan sun bar yankin.
Gwamnatin ta bukaci karfafa hadin gwiwa da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro domin yaki da ‘yan bindiga da sauran laifukan tashin hankali.













































