CJ⁠N ga shugaban CCT: Kada ka yi amfani da muƙaminka wajen yin son kai

CJN Justice Kudirat Kekere Ekun

Babbar jojin Najeriya mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta ja kunnen sabon shugaban kotun ladabtarwa ta ma’aikata (CCT), Mai Shari’a Mainasara Umar, da kada ya yi amfani da ofishinsa don cimma muradunsa na kashin kai.

Mai Shari’a Kekere-Ekun ta yi wannan gargadi ne a ranar Talata a birnin Abuja, bayan ta rantsar da sabon shugaban kotun.

Ta bukaci shi da ya tabbatar da amincewar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nuna gare shi ta hanyar gudanar da shugabanci mai gaskiya da adalci.

Ta ce matsayin da yake rike da shi na buƙatar mutum mai zurfin tunani, wanda ba ya karkata, kuma mai jarumtar yin abin da ya dace ko da kuwa hakan zai shafi manyan mutane.

Ta kuma gargade shi cewa aikin da ke gabansa ba zai kasance mai sauƙi ba, domin wasu daga cikin shari’o’in da kotun za ta yi suna da tasiri sosai a kan amincewar jama’a ga gwamnati.

Karin labari: Babbar jojin Najeriya ta rantsar da sababbin lauyoyi 57 da suka samu matsayin SAN

Mai Shari’a Kekere-Ekun ta shawarce shi da ya rika yanke hukunci bisa gaskiya da doka, ba tare da nuna bambanci ba, tare da tunawa cewa biyayyarsa ta farko ita ce ga yarayyar Najeriya, kundin tsarin mulki da kuma gaskiya, ba ga wani mutum ko ƙungiya ba.

Ta kuma gargade shi da kada ya bari tasirin waje ya rinjayi hukuncinsa, tana mai cewa ya zama wajibi ya tsaya kan gaskiya ba tare da tsoro ko son rai ba, domin hakan ne kawai zai ƙara wa kotun daraja da amincewar jama’a.

A cikin jawabinsa, Mai Shari’a Umar ya gode wa gwamnati bisa amincewar da ta nuna gare shi, tare da tabbatar da cewa zai gudanar da adalci cikin gaskiya, tawali’u da jarumta.

Ya kuma sha alwashin tabbatar da cewa kotun za ta ci gaba da zama abin dogaro wajen aiwatar da hukunci cikin gaskiya da tsari.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa bayan rantsar da sabon shugaban, kotun CCT ta cika da alkalan ta uku, wanda hakan ke ba ta damar ci gaba da sauraron shari’o’in da suka tsaya saboda rashin shugaban kotun.

Sauran mambobin kotun su ne Mai Shari’a William A. Atedze da Mai Shari’a Julie Anabor.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here