Shettima ya bar Abuja zuwa Angola

Shettima departs new 750x430 (1)

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, a ranar Asabar ya bar Abuja zuwa Luanda, babban birnin Angola, domin halartar Taron Musamman na Majalisar Shugabannin Kasashe da Gwamnati na Tarayyar Afirka (AU) na 21.

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Yada Labarai da Sadarwa, Stanley Nkwocha, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce Shettima zai wakilci Shugaba Bola Tinubu a taron.

Nkwocha ya bayyana cewa babban taron zai mayar da hankali kan dabaru masu muhimmanci wajen warware rikici da kuma cigaba da samar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin nahiyar Afirka.

Ya ce Shettima zai hada kai da shugabannin kasashen Afirka da sauran manyan masu ruwa da tsaki da suka taru a babban birnin Angola domin tattauna mafita ta zahiri ga matsalolin tsaro na yanki da karfafa kokarin hadin kai na warware rikici.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar ya ce Najeriya na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen gina zaman lafiya da warware rikici a fadin Afirka dama duniya baki daya.

A cewarsa, ana sa ran Najeriya za ta bayar da gudummawa wajen tattaunawa kan karfafa tsarin nahiyar na hana rikici, warware sabani da kuma kiyaye zaman lafiya.

Nkwocha ya ce Shettima, wanda ke samun rakiyar manyan jami’an tsaro, zai gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a taron, inda zai bayyana matsayin Najeriya kan batutuwan taron.

Ya ce Mataimakin Shugaban Kasar zai sake jaddada kudurin Najeriya na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin nahiyar.

A cewar Nkwocha, Shettima zai dawo Najeriya bayan kammala ayyukan sa a Angola. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here