Najeriya ta bayyana rashin ji dadin ta game da ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkinafaso daga ECOWAS

IMG 20240130 WA0009

Nijeriya ta bayyana bakin cikinta dangane da matakin da kasashen Nijar, Mali da Burkinafaso suka dauka na ficewa daga kungiyar hadin kan kasashen Afrika ECOWAS.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya Francisca K. Omayuli (Mrs) ce ta bayyana haka a wata sanarwa data fitar ranar Litinin.

Najeriya wadda take babba kuma  mai rike da  shugabancin ECOWAS ta dage wajen ganin an dawo da mulkin farar hula  a Nijar, tare da sakin hambararren tsohun shugaban kasar Bazoum Muhammad.

Kazalika sanarwar ta kara da cewa Nigeria ta Kasan ce tana tuntubar dukkan kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS domin warware matsalolin da ake fuskanta a kasashen da akayi juyin mulki.

Sanarwar ta ce Najeriya na ci gaba da bude kofa ga kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar, ta yadda daukacin al’ummar yankin za su ci gaba da cin moriyar tattalin arziki da kimar dimokradiyya da kungiyar ECOWAS ta amince da su.

“Najeriya na kara yin kira ga kasashen duniya da su ci gaba da bayar da goyon bayan su ga kungiyar ECOWAS da kuma hadin gwiwa da hadin kan kasashen Afrika. “

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here