Mata a Kano sun rungumi tuƙa Adaidata Sahu don samun abin dogaro

WhatsApp Image 2025 09 12 at 18.00.10 750x430 (1)

A Kano, an hango mata na tukin Adaidata Sahu ya jawo hankalin jama’a, inda wasu ke kallon abin mamaki ko nishaɗi, yayin da wasu kuma ke nuna rashin amincewa da sabon ci gaban.

A wata hira da SolaceBase TV, wata mai tuki daga Sharada, Fatima Sharif, ta ce sun shiga wannan sana’a ne domin su tabbatar wa da jama’a cewa mata ma za su iya yin aiki da samun abin dogaro kamar maza.

Fatima ta bayyana cewa wannan aikin yafi zaman banza ko dogaro da neman taimako.

Ta ƙara da cewa ta koyar da sauran mata masu sha’awar shiga sana’ar, kuma jama’a da dama suna nuna goyon baya ta hanyar addu’a ko kyaututtuka.

Ta bayyana cewa su na gudanar da harkar cikin tsari: idan fasinja na farko namiji ne, sauran maza ne za su shiga; haka nan idan mace ce, sai mata kaɗai.

Karin labari: Gwamnati ta umurci Dangote da NUPENG su aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a ranar 9 ga satumba

Sai dai ta koka cewa wasu mata basu yarda su hau Adaidata Sahu da mata masu tuki ba, abin da ta ce yana da ban takaici.

Haka nan wasu maza na sukar su da cewa talauci ne ya saka su yin aikin. Amma ta ce yin haka ya fi bara, karuwanci ko sata, domin neman halal ne.

Fatima ta ƙarfafa mata su rungumi ‘yancin dogaro da kai ta kowace irin sana’a da za su iya, tana mai cewa “zamanin ya canza, ba maza kaɗai za su iya ɗaukar nauyin gida ba.”

Ta kuma bukaci gwamnati ta samar da ƙarin damar shiga harkar sufuri domin ba da dama ga mata masu sha’awar shi ga sana’ar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here