Gwamnatin tarayya ta umurci Kamfanin Matatar mai ta Dangote tare da ƙungiyar NUPENG su aiwatar da cikakken yarjejeniyar da aka cimma ranar 9 ga Satumba, 2025, wadda ta tabbatar da ‘yancin ma’aikata na shiga kowace ƙungiya da suke so.
Umarnin ya fito ne daga zama na musamman da aka gudanar a babban ofishin DSS da ke Abuja, tare da halartar Ministar ƙananan Ayyukzan yi, Nkeiruka Onyejeocha, da wakilan NMDPRA, NLC, shugabannin NUPENG da kuma tawagar Kamfanin Dangote ƙarƙashin jagorancin Sayyu Dantata.
Majiyoyi sun ce Gwamnati ta nuna rashin jin daɗi kan zargin cewa jami’an Kamfanin suna cire alamomin NUPENG daga kan motoci, tare da fifita motocin wata ƙungiya mai suna DTCDA, wadda ake ganin Kamfanin ne ya ɗora.
Labari mai alaƙa: DSS ta gayyaci Dangote da NUPENG kan zargin karya yarjejeniya
A cikin yarjejeniyar 9 ga Satumba an amince cewa: ba za a ƙirƙiri ƙungiyoyin da Kamfani ya ɗora ba, rajistar ma’aikata cikin ƙungiya ta kammala tsakanin 9 zuwa 22 ga Satumba, ba za a hukunta ko azabtar da ma’aikata saboda shiga ƙungiya ko yajin aiki ba, sannan duka bangarorin su mika rahoton cigaba ga Ministan Aiki bayan mako guda da kammala shirin.
Gwamnati ta gargadi cewa ba za ta amince da sake karya wannan yarjejeniya ba, tare da jaddada cewa bin ka’idoji ne kaɗai zai kawo zaman lafiya a masana’antar.
A baya NUPENG ta zargi Kamfanin Dangote da karya yarjejeniyar, abin da Kamfanin ya musanta, kuma har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma daga bangarorin biyu kan sabon umarnin Gwamnati.
Vanguard










































