Tagwayen Kano, Hassana da Husaina, da aka haife su a haɗe kuma aka yi musu aiki don raba su a Saudiyya a bara an samu nasara kuma sun dawo gida inda aka tarbe su da farin ciki a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA).
Tagwayen sun tafi Riyadh a watan Oktoba 2023 don cikakken binciken likitoci, inda aka gano suna haɗe a ƙasa da ciki, ƙugu da kashin baya, lamarin da ya sa aikin ya zama mai matuƙar wahala.
Aikin ya gudana a Asibitin Kula da Yara na King Abdullah a Riyadh, ƙarƙashin umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman.
Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Ahmed Al-Admawi, wanda ya tarbe su, ya bayyana wannan nasara a matsayin hujjar jajircewar Saudiyya wajen taimakon al’umma.
Ya ce wannan shi ne aikin raba tagwaye na 65 da shirin Saudi na Siamese Twins Separation Program ya yi cikin shekaru 35, wanda ya riga ya kula da tagwaye sama da 150 daga ƙasashe 25.
Ya ƙara da cewa, ta hannun cibiyar jin kai da taimako ta King Salman, Saudiyya za ta ci gaba da tallafawa ƙasashe, musamman Najeriya da suke da dangantaka ta tarihi da ita.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin ɗaukar nauyin karatun yaran daga firamare har zuwa jami’a, tare da tallafawa iyalinsu da kayan abinci.
Ya godewa Saudiyya bisa wannan taimako da ya kira abin da ya sauya rayuwa.
Mahaifin tagwayen, Alhaji Hassan Isa, cikin hawaye ya nuna godiya ga gwamnatin Saudiyya da kuma gwamnatin Kano bisa kulawa da goyon baya da aka nuna musu tun farko har zuwa dawowarsu.













































