Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar a ranar Talata cewa ya rage yawan kudin rance daga kashi 27.5 cikin ɗari zuwa kashi 27 cikin ɗari, tare da sauya Ma’aunin Manufofin Kuɗi (MPR) da makin 50.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Olayemi Cardoso, ne ya bayyana haka yayin taron kwamitin manufofin kuɗi (MPC) karo na 302 da aka gudanar a ranar Talata.
Kwamitin ya yanke hukuncin a haɗe, inda adadin kudin da dole su bankuna su ajiye wato (CRR) ga manyan bankunan ajiya yankai zuwa kashi 45 cikin ɗari, yayin da ya ci gaba da barin na bankunan ‘yan kasuwa a kashi 16 cikin ɗari.
Sai dai kuma, an bar adadin kadarorin banki da za a iya juyawa nan take wato Liquidity Ratio a daidai kashi 30 cikin ɗari ba tare da an canja shi ba.
Haka kuma, kwamitin ya daidaita adadin dibar da banki ke karbar idan aka ajiye kudi corridor na MPR zuwa +250/-250 domin daidaita ci gaban tattalin arziki da kuma magance hauhawar farashin kaya.
Cardoso ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin rage tsaurin manufofin kuɗi a Najeriya, wacce ita ce babbar ƙasa a nahiyar Afrika, domin ta daɗe tana fama da hauhawar farashin kayayyaki da matsin lambar canjin kuɗi.
Babban Bankin Najeriya ya ce sabon sauyin zai taimaka wajen sassauta yanayin tattalin arziki da kuma bayar da dama ga kasuwanci da masana’antu wajen samun sauƙin cin gajiyar lamuni.













































