Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, a ranar Talata ya mika mutane biyu da aka ceto daga hannun masu garkuwa a Kaduna ga iyalansu, yayin da hukumomin tsaro suka sanar da cafke wasu da ake zargi da aikata manyan laifuka.
Mai kula da Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo Janar Adamu Laka, ne ya mika Khadijah da Fatimah Shehu Magaji ga mijinsu, Alhaji Shehu Magaji, a madadin NSA.
Ya ce nasarar ceto mutanen ta nuna tasirin dabarun da ba na amfani da karfi ba wajen magance matsalar tsaro.
Laka ya bayyana cewa an yi garkuwa da waɗanda aka ceto a ranar 18 ga watan Agusta a Makarfi, Jihar Kaduna, inda aka kaisu Yadi Forest, a cikin Ƙaramar Hukumar Giwa.
Ya ƙara da cewa, yayin da suke tsare, Khadijah ta haifi jaririya, Hafsat, a cikin mawuyacin yanayi, kuma tsawon kwanaki 33 suka sha wahala ƙwarai.
A cewar sa, masu garkuwa da mutanen sun fara neman kudin fansa na naira miliyan 500, daga baya suka rage zuwa miliyan 200. Sai dai bisa tattaunawa da bayanan sirri, an samu nasarar kubutar da su ba tare da biyan fansa ba.
Ya ce an ceto su a ranar 19 ga Satumba, sannan aka mika su ga jami’an gwamnatin Kaduna domin mayar da su ga iyalansu.
Baya ga haka, Laka ya ce jami’an tsaro sun samu gagarumin nasara a wasu ayyuka, inda suka kama Ibrahim Mohammed, da ake kira Alaye, da kuma Adamu Mohammed, waɗanda ake zargi da fashi, garkuwa da mutane, da kisan mutane da dama.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta daure ne da kisan wani ɗan majalisa a Gareywa da kuma kashe wani DPO a Gwagwalada, Abuja, tare da yada ayyukan ta’addanci a jihohin Delta, Kaduna, Kano da Nasarawa.
NAN












































