Hukumar Kula da Masu yi wa Ƙasa hidima, NYSC, ta gargadi masu bautar ƙasa masu son shiga zaɓen 2023 da su kasance ƴan ba-ruwa-na a siyasa.
Mukaddashin darakta Janar na NYSC, Christy Uba ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke jawabi ga mambobin kungiyar a sansanin su na Mbaukwu/Umuawulu da ke karamar hukumar Awka ta Kudu a Anambra a ranar Asabar.
Mukaddashin shugabar ta ce aikin zaben na mai buƙata ne ga mambobin kuma masu son shiga dole ne su nisanci duk wani nau’i na munanan ayyuka da ka iya lalata ingancin zabe ko kimar sa.
Ta ce hukumar NYSC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen miƙa duk wani dan bautar kasa da aka tabbatar da laifin tafka magudin zabe ga jihar domin fuskantar Shari’a
“Idan za ku shiga zaben 2023, to ku sani cewa aiki ne na wucin-gadi, dole ne ku kasance ƴan ba-ruwa-na a kan harkokin siyasa.
“Kada ku shiga ta hanyar da ba ta dace ba, ba dan siyasa ba ne a matsayin ku na masu yi wa ƙasa hidima, za ku iya shiga harkar siyasa nan gaba amma a yanzu, ku ’yan yi wa ƙasa hidima ne.













































