Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, karkashi jagorancin mai shara’a James Omotoshoa a yau Talata, ta aike da wani lauyan yan sanda mai suna Ibrahim Mohammed, zuwa ga hukumar dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annaki domin ta binkice shi, sakamakon shigar da karar Sanata Stella Oduah da ya yi ba tare da izinin hukumar EFCC ba.
Jaridar solacebase ta rawaitu cewa mai shara’a Omotosho ya bada umarnin tuhumar ta sane sakamakon shigar da karar tsohuwar ministan hukumar dake kula da tashi da saukar jiragen sama ta kasa, ba tare da izinin hukumar EFCC ba.
Layan wanda yabar aiki da hukumar ta EFCC tun a watan Nuwambar shekarar 2022, ya yi kuskuren shigar da karar ne da sunan hukumar ta EFCC bayan baya aiki tare dasu.













































