NLC da TUC sun yabawa gwamna Zulum bisa biyansu miliyan N705 na kudin hutu da suke bin gwamnatin jihar

Borno
Borno

Kungiyar kwadago ta NLC tare da kungiyar TUC reshan jahar Barno, a yau Talata sun yabawa gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, bisa sakan musu miliyan N705 na hakokin su na kudin hutu da suke bin gwamnatin jihar.

A wata sanarwa da shugabanin kungiyoyin biyu suka sawa hannu, Yusuf Inuwa na NLC da kuma ta kwaransa na TUC Babayo M. Hamma, sun tabbatar da sakar musu kudin hutu da suke bin gwamnatin jihar ta Barno.

Kungiyoyin biyu sun fitar da sanarwar ne bayan kammala taron da suka gabatar a Maiduguri da ke jihar ta Barno.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here