Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci duk masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da ke neman mukaman siyasa a zaben 2023 da su yi murabus daga yanzu zuwa ranar 31 ga Maris, 2022.
Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Balarabe Abbas Lawal ya fitar.
Ya ce umarnin da aka ba wa masu rike da mukamai na gwamnati da su yi murabus daga nade-naden da aka yi musu a aikin gwamnati ya yi daidai da dokar zabe ta 2022 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu kwanan nan.
Don haka sanarwar ta ce irin wadannan mutane doke su mika takardar murabus dinsu kafin ranar 31 ga watan Maris domin samun damar cimma burinsu na siyasa.
Solacebase ta tuna cewa dokar zabe ta 2022 ta kayyade cewa dole ne wadanda aka nada mukami su yi murabus daga mukamansu kwanaki 30 kafin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar na mukamin da suke nema.












































