Gwamnatin Kano ta rusa cibiyar kasuwanci ta jihar, ta kafa kwamitin riko

DBFEBAA8 C8E5 407C A9BC CE8F581027DC
DBFEBAA8 C8E5 407C A9BC CE8F581027DC

Gwamnatin jihar Kano ta ba da umarnin rusa shugabannin cibiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta Kano (KACCIMA), ba tare da bata lokaci ba, sakamakon rashin shirya sabon zabe.

Musa Tanko, Jami’in Hulda da Jama’a na na ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ranar Laraba a Kano.

Tanko ya ce sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanya hannu kan wannan umarni na rusa.

Ya kuma bayyana cewa, ya zama wajibi a dauki matakin sakamakon gazawar da shugabancin hukumar ta KACCIMA mai ci a yanzu ta shirya sabon zabe mai karbuwa, tun bayan karewar wa’adinsa.

Ya ce tuni Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da kafa kwamitin riko mai mutum tara, karkashin jagorancin fitaccen dan kasuwa Alhaji Lawan Garo.

Ya zayyana wasu daga cikin sharuddan kwamitin da suka hada da; shirya zaben cikin watanni shida, tare da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zauren majalisar.

Ya ce mambobin kwamitin sun hada da Amb. Muktari Gashash, shugaba na biyu, Dr Salim Muhammad, wakilin ma’aikatar kasuwanci, da Alhaji Yakubu Uba.

Sauran kuma sune Alhaji. Tijjani Usman, Alhaji. Kabiru Kura, Hajiya Aisha Baffa da Alhaji Bashir Dado, Bauran Gaya.

A cewar Tanko, Garo, wanda ya yi magana a madadin sauran mambobin kwamitin, ya nuna jin dadinsa ga gwamnati bisa amincewar da aka yi musu; ya kuma yi alkawarin za su yi aiki tukuru domin cimma burin da aka sanya a gaba a cikin wa’adin da aka kayyade.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here