An gano sabuwar hanyar hana zubar jini bayan haihuwa

340310356 1337773853752527 6415256477960345653 n
340310356 1337773853752527 6415256477960345653 n

Masana kimiyya sun yi amanna cewa sun gano wata sabuwar hanya ta bayar da magani domin kare zubar jini bayan haihuwa, wanda aka yi kiyasin cewa yana kashe mata dubu saba’in a duk shekara a duniya.

Maganin mai suna Tranexamic acid, ana amfani dashi ne wajen shawo kan zubar jini bayan haihuwa.

Wakiliyar BBC ta ce yawanci ana bayar da maganin ne ta hanyar allura a jijiya, kuma bayan gwajin maganin a Pakistan da Zambia, masu bincike sun gano cewa maganin na aiki sosai idan har aka yi wa mace allurarsa.

Masana kimiyyar sun ce abin da suka ganon zai yi matukar tasiri musamman a wuraren da ake da karancin asibitoci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here