Kwallon da Aguibou Camara ya ci a karo na biyu, ta baiwa Guinea damar doke Gambia da ci 1-0 a gasar cin kofin mahiyar Afrika.
Sakamakon da ya sa ta ke daf da samun gurbi a zagaye na 16 na karshe.
Dan wasan tsakiya Camara, wanda ke buga wasan kwallon kafa na kungiyarsa a Girka, ya yi nasarar jefa kwallo a ragar Morgan Guilavogui bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci.
Guinea ta kasance kasa mafi kwazo duk da cewa babu tauraron dan wasanta Serhou Guirassy, a dai dai lokacin da suka tashi kunnen doki 1-1 da Kamaru.