Gwamnatin Kano za ta biya ‘yan wasan Para 2023 zuwa Laraba-Bala Sani

Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430
Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430

Daga Aminu Halilu Tudun Wada

Gwamnatin jihar Kano tace za ta biya kudaden Alawus na wasan masu bukata ta musamman da aka kammala a Abuja, Karo na biyu.

Mukaddashin shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano (KSSC) Malam Bala Sani Shehu, ne ya bayyana hakan ya yin zantawar sa da manema Labarai.

Malam Bala Sani, ya kara da cewa Labaran da ake yayatawa cewar tawagar ba a bata komai ba, ba gaskiya bane an bada Miliyan 9 daga cikin kudaden da aka nema don gudanar da gasar.

“Ina mai tabbatar muku da cewar gwamnati za ta biya kowa hakkin sa dangane da ragowar abinda za a bayar tunda hakkin su ne”

A Kano PARA

Karanta wannan:Gwamnatin Kano Zata Biya Diyar Naira Biliyan Uku Ga masu Shagunan  Masallacin Eid 

Mukaddashin ya yabawa tawagar ‘yan wasan jihar Kano bisa nasarorin da suka samu da ‘yan Jaridu bisa gudunmawar su wajen yayata nasarar da kuma aiyyukan da suka shafi wasannin a fadin jihar musamman ma a karkashin hukumar wasannin.

Bala Sani, ya bukaci al’umma da su yi watsi da Labaran kanzon Kurege dangane da yadda ake alakanta tawagar ta jihar Kano a gasar ta PARA Games, Inda ya ce makiya nasarar jihar ne a fannin wasannin.

PARA GAME KANO

Jawabin na shugaban dai ya biyo bayan rahotanni da suka dinga fita a kafafen yada labarai daban-daban, na halin matsin da tawagar ta jihar Kano ta shiga gasar.

Matsin da ake alakanta shi da rashin cikakkun kudaden gudanarwa da kuma rashin kudin Alawus ga ‘yan wasa, jami’an su, masu horar dasu, ma’aikatan hukumar.

An dai kammala gasar Wacce aka fara daga Ranar 8 zuwa 14 ga Disamba, mai taken ‘Abuja Para Games 2023’.

Gasar dai ita ce karo na biyu.Inda jihar Kano duk da kalubalen kudaden ta karkare a mataki na uku, da yawan Lambar Zinare 15, sai Azurfa 12 da Tagulla 17.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here