Tsohon gwamnan jihar Anambra Dakta Chukwuemeka Ezeifa, ya rasu.
A cewar wata sanarwa Chif Rob Ezeifa, ya fitar ranar Juma’a a madadin iyalan marigayin, yace Ezeifa ya rasu ranar alhamis a asibitin tarayya da ke Abuja.
Karanta wannan:Kwamishinan shari’a na jihar Rivers ya ajiye aiki
An haifi Dakta Ezeifa a ranar 20 ga watan Nuwambar 1938, ya taba kasancewa gwamnan jihar Anambra a tsakanin watan janairun 1992 zuwa Nuwambar 1993.