Kotun koli ta Najeriya ta bayar da umarnin a ci gaba da shari’ar tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, tare da ’ya’yansa biyu da wasu mutane, kan zargin damfarar Naira Biliyan 1.35 a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja.
Kwamitin alkalan kotun koli su biyar sun yanke wannan hukunci ne baki ɗaya a cikin hukuncin daukaka kara biyu da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Kudi EFCC ta shigar, inda kotun ta goyi bayan hukuncin kotun farko da ta ce wadanda ake tuhuma suna da amsa da za su bayar a gaban shari’a.
Kotun koli ta soke hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta yanke a baya wanda ya amince da bukatar babu shari’a da Lamido da sauran wadanda ake tuhuma suka shigar, tare da watsar da tuhume-tuhume 37 bisa hujjar rashin hurumin Kotun Tarayya ta Abuja.
A hukuncin jagora, Mai shari’a Abubakar Umar ya tabbatar da hukuncin Mai shari’a Ijeoma Ojukwu na Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ya yi watsi da bukatar babu shari’a da Lamido da sauran wadanda ake tuhuma suka shigar, tare da umartar su shiga gabatar da kariyarsu.
A cikin tuhume-tuhume 37 da EFCC ta gabatar, an zargi Sule Lamido da cin zarafin mukaminsa a matsayin gwamna daga shekarar 2007 zuwa 2015, inda ake zargin ya aikata wankiyar kudade da aka ce ya karɓa a matsayin rashawa daga kamfanonin da aka ba kwangiloli a Jihar Jigawa a karkashin shugabancinsa.
Sauran wadanda ake tuhuma tare da Lamido sun hada da ’ya’yansa biyu Aminu da Mustapha, Aminu Wada Abubakar, da kamfanoninsu Bamaina Holdings Limited da Speeds International Limited.
A wani hukunci na daban, kotun koli ta kuma yi watsi da daukaka karar Aminu Sule Lamido kan hukuncin da aka yanke masa na kin bayyana Dala Dubu Arba’in a filin jirgin sama, inda kotun ta tabbatar da hukuncin da aka yanke masa da umarnin kwace kashi 25 cikin 100 na kudin da bai bayyana ba ga gwamnatintarayya.













































