Ɗa na ya sauya sheƙa zuwa APC – Atiku

Atiku lalala

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, wanda kuma mamba ne na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi martani kan matakin ɗansa Abba Abubakar na komawa jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa matakin na ɗan nasa na ƙashin kansa ne.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a ranar 15 ga Janairu, Abba Abubakar ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC domin bayar da gudummawa wajen sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu, wanda ya fafata da mahaifinsa a zaɓen 2023.

Haka kuma Abba ya sanar da sauya sunan ƙungiyarsa ta siyasa da aka kafa a 2022 daga Atiku Haske Organisation zuwa Haske Bola Tinubu Organisation, alamar cikakken sauyin alkiblar siyasar ƙungiyar.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya jaddada tsayuwarsa kan ƙa’idojin dimokuraɗiyya, inda ya nuna girmamawa ga ’yancin haɗin kai da zaɓin siyasa na ’yan uwansa, kamar yadda yake girmama na dukkan ’yan Najeriya.

Ya bayyana cewa a tsarin dimokuraɗiyya irin wannan zaɓi ba abin mamaki ba ne ko tashin hankali, ko da kuwa siyasa da dangantakar iyali sun haɗu, tare da nuna cewa ba ya tilasta wa ’ya’yansa ko ’yan ƙasa yin wani zaɓi da ya saɓa wa lamirinsu.

Labari mai alaƙa: Ɗan Atiku ya fice daga PDP zuwa APC, tare da nuna goyon baya ga Tinubu

Duk da amincewarsa da sauyin siyasar ɗansa, Atiku ya sake bayyana tsayayyen adawarsa da jam’iyyar APC, inda ya nuna cewa abin da ya fi damunsa shi ne halin mulki da matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ke addabar jama’a.

Atiku Abubakar ya tabbatar da ci gaba da jajircewarsa a sahun adawa, inda ya nuna aniyarsa ta haɗa kai da masu ra’ayi iri ɗaya domin kifar da jam’iyyar mai mulki tare da samar wa ’yan Najeriya wani sahihin zaɓi da zai kawo sauƙi, fata da ci gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here