Zaben cike gurbi gwaji ne na nasarar APC a 2027 – Gwamna Yusuf

Abba Kabir Yusuf Abba 387x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana sakamakon zaben cike gurbin Dawakin Kudu da Warawa na Majalisar Tarayya a matsayin gwaji na nasarar da Jam’iyyar APC ke sa rai a zaben 2027 da ke tafe.

Bayanin na kunshe a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Lahadi.

Gwamna Yusuf ya ce yawan masu jefa kuri’a da kuma gudanar da zaben cikin lumana a fili ya nuna cewa mutane har yanzu suna goyon bayan APC da tsare-tsarenta

Ya ce an gudanar da zaben cikin ‘yanci, adalci da aminci, wanda ya nuna zabin gaskiya na masu jefa kuri’a.

Gwamnan ya yabi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) bisa gudana da aikin cikin nasara kuma ya yaba wa hukumomin tsaro bisa tabbatar da yanayi da ya dace kafin, yayin da kuma bayan zaben.
A cewarsa, yadda aka gudanar da zaben da sakamakonsa sun kara karfafa amincewar jama’a ga tsarin dimokuradiyya a Najeriya.

Gwamna Yusuf ya taya dan takarar APC murna kan nasararsa kuma ya ba shi shawara ya ci gaba da jajircewa wajen cika burin al-ummarsa ta hanyar wakilci mai inganci da ma’ana.

Ya ce sakamakon zaben ya aika sako mai karfi cewa APC har yanzu ita ce babbar jam’iyyar siyasa a Jihar Kano kuma tana cikin shiri don samun manyan nasarori a zabukan da ke tafe.

Gwamnan ya kuma ya caccaki Jam’iyyar NDC kan rashin gabatar da dan takara a zaben cike gurbin, inda ya bayyana jam’iyyar a matsayin kungiyar siyasa wadda ba ta da tsari mai karfin tushe.

Ya ce shawarar NDC ta kaurace wa fafatawar ta samo asali ne daga tsoron kaye da ba makawa, ganin cewa ta san ba ta da goyon bayan da ake bukata don fafatawa da APC.

Gwamna Yusuf ya ce zaben cike gurbin ya tona asirin raunin abokan adawa a jihar kuma ya kara nuna yadda mutane ke kara karbar APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here