Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Asabar ya yi ganawar sirri da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da dan takarar gwamnan Jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Dr Jamil Isyaku Gwamna, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Ganawar ta mayar da hankali kan batutuwa masu alaka da ci gaba da aka yi a Jihar Gombe da kuma kiyaye nasarorin da aka samu a karkashin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Wata sanarwa da Ibrahim Sani Shawai, Kakakin Dr Jamil Isyaku Gwamna, ɗldan takarar gwamnan APC na Jihar Gombe, ya fitar a ranar Lahadi ta ce tattaunawar wani bangare ce na ci gaba da tuntubar manyan mutane domin tabbatar da ci gaba a mulki, karfafa gyare-gyaren da ake yi da kuma ci gaba da hangen nesan samar da Jihar Gombe mai yalwa da bunkasar tattalin arziki.
Bayan taron, Gwamna Yahaya ya yi amfani da damar ya gabatar da Dr Jamil Isyaku Gwamna ga Shugaban Kasa a matsayin dan takarar gwamnan APC na Jihar Gombe.
Wannan gabatarwar ba wai nasara ba ce kawai, alama ce mai karfi ta hadin kai, ci gaba, da himma wajen tabbatar da cigaban Jihar Gombe mai dorewa a karkashinjam’iyyar APC.
Ana kallon taron a matsayin wani manuni ga himmar da shugabancin APC a matakin kasa da jihar wajen kare ci gaban da aka samu a Gombe da tabbatar da sauyin mulki cikin sauki wanda zai dogara kan ci gaba, kwanciyar hankali da mulki mai inganci.











































