Buhari ya sabunta nadin Manajan Daraktan bankin masana’antu

6044FEF8 8436 4E0B AB9B 909AE253E2BC
6044FEF8 8436 4E0B AB9B 909AE253E2BC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabunta nadin Mista Kayode Pitan a matsayin Manajan Daraktan Bankin Masana’antu (BOI) na tsawon shekaru biyar.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Ifedayo Sayo, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce sabon nadin wanda zai fara aiki daga ranar 27 ga Mayu, 2022, an bayyana shi ne  ta cikin wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha mai kwanan wata 11 ga Maris, 2022.

Haka kuma, shugaban ya amince da sabunta nadin Alhaji Dikko Aliyu Abdulrahaman a matsayin shugaban bankin na tsawon shekaru biyar na karshe daga ranar 27 ga Mayu, 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here