Yajin aikin SSANU da NASU ya dakatar da ayyuka a BUK

BUK 4 300x145 1
BUK 4 300x145 1

Ayyuka a Jami’ar Bayero ta Kano sun tsaya cak a ranar Litinin yayin da kungiyoyin ma’aikatan da ba malamai ba suke ci gaba da yajin aikin gama-gari na sai-baba-ta-gani, inda suke neman karin albashi na kaso 45 da kuma cikakken aiwatar da yarjejeniyar 2009.

Kungiyar reshen Jami’ar Bayero ta Kano, ya sanar da shigarsa cikin yajin aikin da ke gudana a fadin kasa.

Sakataren Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), a BUK, Dr. Nura Garba, ya bayyana hakan a wata hira da yayi da SolaceBase ranar Litinin, yana mai cewa shawarar ta biyo bayan umarni daga Kwamitin Hadin Gwiwa (JAC), wanda ya umurci mambobi da su fara yajin aikin sai-baba-ta-gani daga watan Mayu 2026.

Dr. Garba ya bayyana cewa an cimma wannan shawarar ne bayan wani taron gaggawa na JAC da aka gudanar a Abuja ranar 18 ga Afrilu, inda aka tattauna kan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen kammala yarjejeniyar sake tattaunawa da kungiyoyin ma’aikatan da ba malamai ba.

A cewarsa, yayin da gwamnati ta yi nasarar sake tattaunawa da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta (ASUU), ciki har da amincewa da karin albashi na kaso 40, an bai wa ma’aikatan da ba malamai ba karin kaso 30 kawai.

“Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta kammala wannan sake tattaunawar kuma ta kara wa ma’aikatan da ba malamai ba kaso 40 din da aka ba ASUU,” in ji shi.

Jami’in SSANU ya yi gargadin cewa idan halin da ake ciki ya ci gaba, ayyukan gudanarwa a fadin jami’o’in Najeriya za su lalace matuka, yana mai jaddada cewa yajin aikin cikakke ne kuma na sai-baba-ta-gani har sai an biya bukatunsu.

Haka kuma, Shugaban NASU, Kwamared Abdullahi Nasiru Abdulrafiu ya shaida wa jaridar SolaceBase cewa shiga yajin aikin umarni ne daga hedkwatar kungiyar ta kasa.

SolaceBase ta ruwaito cewa Kwamitin Hadin Gwiwa (JAC), wanda ya kunshi kungiyoyin ma’aikatan ilimi da wadanda ba na ilimi ba a jami’o’in Najeriya, ya dade yana fafutukar ganin an inganta jin dadin rayuwa da kuma daidaito tsakanin ma’aikatan jami’a.

Bambance-bambancen tsarin albashi da jinkirin aiwatar da yarjejeniyoyin sun saba haifar da yajin aiki a fannin, wanda sau da yawa ke haifar da tsaiko mai tsawo a kalandar karatu.

Yajin aikin da ake ciki a yanzu ya nuna ci gaba da takun saka tsakanin kungiyoyin jami’o’i da Gwamnatin Tarayya, lamarin da ke tayar da sabbin damuwa game da kwanciyar hankali a tsarin manyan makarantun Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here