Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ce ta yi nasarar rufe makarantu da cibiyoyin ilimi dake bada shedar Digiri 62 ba bisa ka’ida ba a kasar nan.
Hukumar ta kuma ce ta rufe wani sansanin masu yiwa kasa hidima na bogi a yunkurinta na dakile cin hanci da rashawa a fannin ilimi.
Shugaban hukumar Farfesa Bolaji Owasanoye ne ya bayyana haka a taron tattaunawa da matasa kan cin hanci da rashawa a manyan makarantun da aka gudanar a Abuja.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ICPC ce ta shirya wannan gangamin tattaunawa da mambobin kungiyar Vanguards da ke yaki da cin hanci da rashawa daga manyan makarantu biyar da ke abuja.
Owasanoye, wanda ya samu wakilcin Uwargida Hannatu Mohammed kuma mamba a hukumar ICPC mai kula da matasa, ta ce tuni hukumar ta gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
A cewarsa, cin hanci da rashawa na matukar yin illa ga ingancin ilimin kowacce al’umma, domin babu wata al’umma da za ta ci gaba idan ilimin kasar baida inganci.
Ya ce hukumar ta ICPC ta kafa jami’an tsaro na yaki da cin hanci da rashawa a makarantu domin tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa a bangaren ilimi musamman a manyan makarantu.
A jawabin da ya gabatar, Farfesa Williams Barnabas, mataimakin shugaban jami’ar Bingham, ya ce dole ne a mayar da tsarin ilimin Najeriya don ba da gudummawa sosai ga cigaban kasa.
Barnaba ya ce cin hanci da rashawa a manyan makarantu yana tasiri matuka kan ingancin ilimi.













































