Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi tattaki zuwa kasashen Turai kan harkokin kasuwanci.
Cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin labarai Paul Ibe ya fitar ranar Talata a Abuja.
Sanarwar ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi bulaguron ne da daddare domin ganawa da abokan huldar sana’ar sa na kasuwanci sakamakon kullen COVID-19 a duniya da kuma yadda za a farfado da tattalin arziki.
Sanarwar ta ce, ziyarar za ta kuma maida hankali kan shawarwarin karshe don fadada aikin samar da tattalin arzikin bai daya dan inganta harkaokin kasuwanci.













































