Zargin almundahanar kuɗi: Malami da ɗansa, har ma da wanda ake karar su tare sun nemi beli bayan an gurfanar da su a gaban kotu

Abubakar Malami (1)

Tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Barrista Abubakar Malami SAN, tare da ɗansa da wani wanda ake tuhuma tare da su, sun nemi beli a ranar Talata bayan an gurfanar da su kan zargin aikata laifukan halasta kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

Mutanen uku, ta bakin lauyansu Joseph Daudu SAN, sun gabatar da buƙatar belin ne ta baki bayan lauyan hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC, Ekele Iheanacho SAN, ya nemi dage shari’a domin ba da damar mayar da martani kan takardun neman beli da aka shigar a madadin waɗanda ake tuhuma.

Lamarin ya faru ne bayan waɗanda ake tuhuma sun musanta laifin tuhume-tuhume 16 da EFCC ta shigar a kansu, inda Iheanacho ya kuma nemi a sanya ranar fara shari’a domin gabatar da shaidun da hukumar ke da su a kan mutanen.

Lauyan EFCC ya bayyana cewa an karɓi takardun neman beli ne a jiya da misalin ƙarfe uku na rana, kuma hukumar na buƙatar lokaci domin amsa buƙatar, tare da neman yardar kotu ta ba da ranar yin hakan.

Sai dai Daudu ya jaddada cewa duk da shigar da takardar neman beli a rubuce, doka ta ba shi damar yin buƙatar ta baki, inda ya jingina da wani hukuncin kotu na shekarar 1995 da ya shafi shari’ar Abiola da Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.

Bayan sauraron hujjojin lauyoyin ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Nwite ya ajiye shari’ar domin yanke hukunci kan buƙatar belin da aka gabatar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa a cikin tuhumar da aka yi lamba FHC/ABJ/CR/700/2025, EFCC ta sanya sunan tsohon ministan, Hajia Bashir Asabe da Abubakar Abdulaziz Malami a matsayin waɗanda ake tuhuma na farko, na biyu da na uku.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here