Kotu ta tsare Malami, ɗansa da wanda ake tuhuma tare da su a gidan gyaran hali na Kuje

AGF Malami

Kotun tarayya mai sauraron manyan laifuka da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Barrista Abubakar Malami SAN, tsohon Antoni Janar na Tarayya, tare da ɗansa da wani wanda ake tuhuma tare da su, a gidan gyaran hali na Kuje, har sai an saurari buƙatar belinsu.

Mai shari’a Emeka Nwite ya yanke wannan hukunci ne bayan lauyan masu tuhuma, Joseph Daudu SAN, ya gabatar da buƙatar beli ta baki, inda kotu ta nuna cewa adalci da ka’idojin sauraron ƙara yadda ya dace na buƙatar a bai wa ɓangaren masu gabatar da ƙara damar amsa buƙatar belin da aka shigar tun da farko.

Kotu ta tabbatar da cewa an riga an shigar da takardar neman beli daga ɓangaren masu kare kai, kuma an isar da ita ga ɓangaren masu gabatar da ƙara, tare da jaddada cewa ba za a iya janye wannan buƙata ba a wannan mataki.

Labari mai alaƙa: Zargin almundahanar kuɗi: Malami da ɗansa, har ma da wanda ake karar su tare sun nemi beli bayan an gurfanar da su a gaban kotu

Mai shari’a ya bayyana cewa duk da ikon da kotu ke da shi na bayar da beli, dole ne a yi hakan ne bayan masu gabatar da ƙara sun mayar da martani kan buƙatar belin, domin guje wa tauye haƙƙin sauraron ƙara yadda ya dace.

Kotu ta nuna cewa bayar da beli kafin amsar ɓangaren masu gabatar da ƙara zai zama tamkar shirya musu tarko, wanda hakan zai karya ka’idojin adalci a shari’a.

Bisa wannan dalilai, kotu ta bayar da umarnin tsare Malami, Hajia Bashir Asabe da Abubakar Abdulaziz Malami a gidan gyaran hali na Kuje, tare da dage shari’ar zuwa lokacin da za a saurari buƙatar belin.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta shigar da tuhuma mai lamba FHC/ABJ/CR/700/2025, inda ta sanya tsohon ministan, Hajia Bashir Asabe da Abubakar Abdulaziz Malami a matsayin waɗanda ake tuhuma na farko, na biyu da na uku a shari’ar halasta kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here