Sojoji 16 za su fuskanci shari’a bisa zargin rashin ɗa’a -Shalkwatar tsaro

nigerian army training

SHalkwatar tsaro ta Ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa sojoji 16 za su fuskanci cikakken shari’ar soja saboda rashin ɗa’a da karya ƙa’idojin aiki.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro, Manjo Janar Tukur Gusau, ya fitar ranar Asabar, rundunar ta ce an kama jami’an da abin ya shafa, yayin da bincike ke ci gaba don gano irin girman laifin da suka aikata.

Gusau ya ce wasu daga cikin jami’an sun daɗe suna ƙarƙashin bincike bisa laifuka daban-daban, inda wasu ma tuni ake yi musu shari’a.

Ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa mafi yawan waɗannan jami’an suna nuna rashin jin daɗi ne saboda rashin samun ci gaba a matsayi, sakamakon rashin cin nasara a jarrabawar karin girma, da sauran dalilai.

Bincike ya gano cewa matsalolinsu sun samo asali ne daga rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da karin girma da matsayi da wasu batutuwa na ciki.

Karanta: Hedkwatar tsaro ta ƙasa Ta Bayyana Gaskiya kan Batun Nada Mukaddashin Hafsan Sojin Kasa 

Ya ƙara da cewa waɗanda bincike ya tabbatar da laifinsu za su fuskanci cikakken hukunci bisa ƙa’idojin soja domin tabbatar da adalci da kiyaye kwararru a cikin rundunar.

DHQ ta kuma jaddada cewa wannan mataki ba wani abu bane illa tsarin yau da kullum na tabbatar da ɗa’a, biyayya da mutunta doka a cikin rundunar.

Rahotanni sun nuna cewa irin waɗannan matakan hukunta jami’an ba sabon abu ba ne a rundunar soja ta Najeriya, domin a wasu lokuta ana ɗaukar mataki kan sojoji bisa laifin tayar da tarzoma, gudu daga aiki, da sauran abubuwan da ke sabawa dokokin soja.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here