Ban taɓa danganta Buhari da Boko Haram ba – Jonathan

Former President Goodluck Jonathan 750x430

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa ya taɓa zargin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari da alaƙa da Boko Haram, yana mai cewa rahotannin da ke yawo an ƙirƙire su ne kuma ba su da tushe.

Jonathan ya bayyana hakan ne bayan kalamansa a wajen ƙaddamar da littafin tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), inda wasu kafafen yaɗa labarai suka fassara kalamansa ta hanyar da ta kau da hankali daga ainihin ma’anar su.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen yaɗa labarai, Ikechukwu Eze, ya fitar, Jonathan ya ce ba a wani lokaci ya nuna, ko ya yi nuni, ko ya taɓa zargin cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba.

Labari mai alaƙa: Boko Haram ba ta taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakani ba, Jonathan ya yi ƙarya – Garba Shehu

Ya bayyana cewa maganganunsa sun shafi yadda Boko Haram ta yi amfani da yaudara da ruɗani a farkon zamaninta don tayar da rikici a siyasar Najeriya.

Jonathan ya ce a lokacin, ‘yan ta’addan suna ambaton sunayen mutane da ake girmamawa, ciki har da Buhari, domin rarraba kawunan ‘yan siyasa da kuma rage amincewar jama’a da gwamnati.

Ya tambayi masu yaɗa labarin karya da cewa, “Idan har Boko Haram ta zaɓi Buhari a matsayin mai shiga tsakani, me ya sa ba ta daina ta’addanci lokacin da ya zama shugaban ƙasa ba?”

Ya ƙara da cewa, shi da Buhari duka sun yi ƙoƙari wajen yaƙar ta’addanci a lokacin mulkinsu, suna da manufa ɗaya ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar nan.

Tsohon shugaban ƙasar ya roƙi ‘yan Najeriya da su yi watsi da duk wani yunƙuri na siyasantar da maganarsa ko kuma karkatar da ita don yin tasiri a siyasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here