Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya da su koyi rayuwa cikin haɗin kai duk da bambancin addinai, yana mai cewa addini ya kamata ya zama hanyar haɗin kai, ba rarrabuwar kai ba.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Asabar a birnin Jos, Jihar Filato, yayin bikin jana’izar Lydia Yilwatda, mahaifiyar Nentawe Yilwatda, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa.
Shugaban ƙasar ya ce dukkan al’amuran duniya suna ƙarƙashin ikon Allah, kuma kowane mutum, ko Musulmi ko Kirista, yana bautawa Ubangiji guda ɗaya.
Karin labari: Ban taɓa danganta Buhari da Boko Haram ba – Jonathan
Tinubu ya bayyana yadda bambancin addini bai taɓa kawo matsala a cikin gidansa ba, inda ya ce shi Musulmi ne, yayin da matarsa, Oluremi Tinubu ta ƙasa fasto ce.
Ya ce aurensu na zama abin koyi ne ga yadda Najeriya za ta iya samun haɗin kai idan aka mayar da hankali kan ƙauna da mutunta juna, maimakon bambance-bambance.
Shugaban ƙasar ya kuma yi addu’a ga marigayiya Lydia Yilwatda, wadda ta rasu a watan Agusta tana da shekara 83, yana bayyana ta a matsayin mace mai ƙwarin gwiwa, imani, da hidima ga jama’a.











































