Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta ankarar da gwamnatin tarayya kan matakin da wasu manyan yan kasuwa masu hada-hadar fetur marasa kishin kasa ke shirin dauka na kara farashin albarkatun mai don haddasa matsalar tsadarsu.
Shugaban kungiyar ta IPMAN na Kano, Alhaji Bashir Danmallam, ne ya yi zargin ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau Jumaa nan Kano, aka aike wa Solacebase.
Sanarwar ta zargi wasu daga cikin irin wadannan yan kasuwa wadanda ke da wuraren ajiye mai inda suke niyya kara farashin man fetur daga Naira 148 akan kowacce lita guda zuwa Naira 153 ko kuma Naira 155 a kowace lita, tun ranar Juma’ar da ta gabata.
Sanarwar ta ce,” Kungiyar ta ga ya zama dole ta fadakar da Gwamnati don kada ta zargi mambobinta idan sun kara farashin mai saboda ba za su sayar da shi yadda za su yi asara ba.”
IPMAN na zargin wasu masu gidajen ajiye mai masu zaman kansu da kokarin yi wa gwamnatin tarayya zagon kasa ta hanyar kara farashin ta bayan fage, duk da cewa gwamnati ba ta kara farashin ba.
Muna kuma yin kira ga hukumar NNPC da ta binciki lamarin kamar yadda wasu daga cikin masu wuraren ajiyar mai masu zaman kansu tun daga ranar Jumaar da ta gabata suka yi karin farashin, Mun san gwamnatin tarayya ce kadai ke shigo da mai ba masu wuraren ajiya masu zaman kansu ba, inji shi.
Kamar yadda a yanzu haka rumbunan adana mai masu zaman kansu a Warri da Calabar da Lagos da Oghara sun kara farashin su, Muna fatan hukumomin NNPC za su yi bincike su shiga tsakani, in ji Danmalam a cikin sanarwar.
” Ya ce kungiyar IPMAN ba za ta nade hannayenta ba kuma ba za ta kyale irin wadannan masu manyan yan kasuwa su tsunduma najeriya cikin hauhawar farashin da ba dole ba yayin da a koda yaushe jama’a ke zargin mambobin mu wajen da karin farashin man fetur. ”
Kungiyar IPMAN ta ankarar da gwamnatin tarayya kan karin farashin fetur
Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta ankarar da gwamnatin tarayya kan matakin da wasu manyan yan kasuwa masu hada-hadar fetur marasa kishin kasa ke shirin dauka na kara farashin albarkatun mai don haddasa matsalar tsadarsu.
Shugaban kungiyar ta IPMAN na Kano, Alhaji Bashir Danmallam, ne ya yi zargin ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau Jumaa nan Kano, aka aike wa Solacebase.
Sanarwar ta zargi wasu daga cikin irin wadannan yan kasuwa wadanda ke da wuraren ajiye mai inda suke niyya kara farashin man fetur daga Naira 148 akan kowacce lita guda zuwa Naira 153 ko kuma Naira 155 a kowace lita, tun ranar Juma’ar da ta gabata.
Sanarwar ta ce,” Kungiyar ta ga ya zama dole ta fadakar da Gwamnati don kada ta zargi mambobinta idan sun kara farashin mai saboda ba za su sayar da shi yadda za su yi asara ba.”
IPMAN na zargin wasu masu gidajen ajiye mai masu zaman kansu da kokarin yi wa gwamnatin tarayya zagon kasa ta hanyar kara farashin ta bayan fage, duk da cewa gwamnati ba ta kara farashin ba.
Muna kuma yin kira ga hukumar NNPC da ta binciki lamarin kamar yadda wasu daga cikin masu wuraren ajiyar mai masu zaman kansu tun daga ranar Jumaar da ta gabata suka yi karin farashin, Mun san gwamnatin tarayya ce kadai ke shigo da mai ba masu wuraren ajiya masu zaman kansu ba, inji shi.
Kamar yadda a yanzu haka rumbunan adana mai masu zaman kansu a Warri da Calabar da Lagos da Oghara sun kara farashin su, Muna fatan hukumomin NNPC za su yi bincike su shiga tsakani, in ji Danmalam a cikin sanarwar.
” Ya ce kungiyar IPMAN ba za ta nade hannayenta ba kuma ba za ta kyale irin wadannan masu manyan yan kasuwa su tsunduma najeriya cikin hauhawar farashin da ba dole ba yayin da a koda yaushe jama’a ke zargin mambobin mu wajen da karin farashin man fetur.”