Hukumar tattara kudaden haraji ta kasa FIRS, ta ce akwai bukatar fara karbar kudaden haraji kan kayayyakin aikin gina hanyoyi a kasar nan domin bangaren da ba na yau da kullun ya ba da tasa gudummawa wajen gina al’umma.
Shugaban hukumar ta FIRS, Muhammad Mamman Nami, ne ya bayyana hakan jiya Alhamis, yayin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, karkashin jagorancin shugaban ta, Chris Isiguzo, a ofishin sa da ke birnin tarayya Abuja.
Nami ya ce, shirin harajin ababen more rayuwa na hanya da hukumar tarayya za ta gudanar, zai bai wa gwamnati isassun kudade don gina hanyoyi da gyara su tare da samar da tsaron da ake bukata na hanyoyin kasar nan.
A cewar shugaban, “Abu mai mahimmanci da ake buƙata shi ne a cikin tsarin tallafin Kayayyakin aikin hanya da Najeriya ke buƙata don gyara hanyoyin mu da kuma kawo ɓangaren da ba na yau da kullun ba a cikin harajin.”
Haka kuma ya ce, ” A wasu nahiyoyi da dama, masu shigar da irin wadannan kaya na biyan harajin don haka bai kamata a ɗauki hakan a matsayin ƙarin nauyi ga ‘yan Najeriya ba saboda yana da damar inganta rayuwar mu baki ɗaya.”
Da yake karin haske, Nami ya bayyana cewa a halin yanzu tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne kacokan kan kudaden shiga da ba na man fetur ba don sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa na biyan albashi da samar da ababen more rayuwa ga al’ummar Najeriya.
A cewarsa, ba tare da biyan haraji ba, gwamnatoci a dukkan matakai ba za su iya sauke nauyin da ke kansu ba ga al’ummar da suka jefa wa shugabanni kuri’a.
Ya jaddada cewa kudin haraji kuma yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hanyoyin sun kasance cikin aminci kuma ko da yaushe suna cikin yanayi mai kyau.
Haka kuma ya kara da cewa ya ‘’Kamata hauhawar farashin danyen mai ya yi tasiri matukar kan harajin ribar man da kamfanonin da ke hako mai ke biya, Sai dai hakan ba ta samu ba saboda wasu dalilai.’’ in ji shi.
Da yak jawabi tun da fari, Chris Isiguzo, ya ce, ziyarar kungiyar, wani bangare ne na kudurinsa na shigar da muhimman cibiyoyi a matsayin manyan masu ruwa da tsaki a matsayin hanyar da za ta kawo ci gaban kasa baki daya.
Shugaban NUJ ya bayyana hukumar ta FIRS a matsayin muhimmiyar cibiya a Najeriya, yana mai cewa, “Akwai buƙatar bai wa hukumar nan duk tallafin da take buƙata musamman a wannan lokacin da Najeriya ke fama da ƙalubalen tsaro da wanda annobar Covid-19 ta kawo baya ga matsalar hada-hadar harkokin kasashen duniya har ma da matsalolin da ke faruwa sakamakon rikice-rikicen da ake samu sakamakon sabani siyasa.













































