Matan Zamfara masu zanga-zanga sun rufe hanyar Gusau zuwa Kaduna

protest
protest

Wasu ɗaruruwan mata a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, sun tare hanyar Gusau zuwa Kaduna a wani mataki na zanga-zanga kan hare-haren da ƴan bindiga ke ci gaba da kaiwa, duk da matakan tsaro da gwamnatin jihar ta ce ta dauka.

Babbar hanyar ta Gusau zuwa Kaduna ta haɗa jihar zuwa wasu jihohi da dama na Arewa da na yankin Kudancin Najeriya.

Matan sun ɗauki yaransu da kayansu sun zauna a kan hanya tare da hana masu ababen hawa wucewa lamarin da ya haifar da dakatar da zirga-zirga ga ɗaruruwan masu ababen hawa.

Wata cikin matan da ta bayyana sunanta Sadiya, ta shaida wa jaridar PUNCH cewa, sun yanke shawarar fitowa don yin zanga-zanga saboda a koda yaushe ƴan fashin daji suna kai musu hari da yi musu fyade kuma babu wani mataki da jami’an tsaro suka dauka na kare su.

Sadiya ta ce, “Mun tare hanya ne domin mu jawo hankalin gwamnati da jami’an tsaro su kawo mana dauki.”

Wata mata, mai suna Talatu Sani, ta ce, ta bar ƙauyen su Cediya saboda ɓata garin suna zuwa ƙauyen don yi wa mata fyade da sace abinci da dabbobin su.

“Dole ne in shiga cikin zanga-zanga saboda hukumomi ba sa yin wani abu don kare mu daga wannan hali na rashin tabbas.”

Duk ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar SP Mohammed Shehu ya ci tura kasancewar bai ɗauki kiran wayar da aka yita yi masa ba.

The Punch

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here