Hukumar NRC ta tabbatar da kai harin Bom akan layin dogo na Abuja zuwa Kaduna

MD NRC Fidet Okhiria1
MD NRC Fidet Okhiria1

Hukumar kula da sifurin jiragen ƙasa ta Najeriya NRC, ta tabbatar da kai harin Bom kan layin dogo na Kaduna zuwa Abuja, wanda yayi sanadiyyar lalata shi da yammacin jiya Laraba da kuma safiyar yau Alhamis inda har kawo yanzu ba a kai ga gano waɗanda suka kai harin ba.

A cewar hukumar tuni aka fara bin matakan tabbatar da cewa an shawo kan matsalar.

A ganawarsa da jaridar Tribune ta Interne, Manajan Darakta hukumar ta NRC Injiniya Fidet Okhiria ya bayyana cewa abubuwan fashewar sun lalata hanyoyin jirgin kasan a wani wuri tsakanin Dutse da Rijana.

Ya ce, “Akwai fashewar abubuwa a kan hanyar jirgin kasa a wani yanki kusa da Rijana da Dutse a daren jiya, kuma fashewar ta yi sanadiyyar lalata layin dogon.

“A halin yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an dawo da ayyukan jirgin daga Kaduna zuwa Abuja,”

Da aka tambaye shi ko akwai harbe-harbe da aka nufi direba da tankin jirgin, sai ya ce, “Babu wani abu makamancin haka, Abun fashewa ne kawai da aka sanya a kan hanyar.

Ya ƙara da cewa “Shin kuna sane da cewa har ma mun gudanar da aikin jirgin ƙasa yau da safe? A halin yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an maido da cikakken ayyukan jirgin kasa a wannan hanyar. ”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here