Kungiyar mata manoma ta kasa WOFAN, ta tallafa wa kananan masu kamfanoni 100 da kayan fara sana’a da kayan abinci, don tunawa da ranar abinci ta duniya ta bana domin rage wahalhalu da talauci a wasu yankunan karkara na jihar Kano.
A cewar babbar daraktar kungiyar ta WOFAN Hajiya Salamatu Garba, sun yi rabon ne a yankunan Gaida, Yan kusa Kadawa Gargai da Chiromawa da duk a jihar Kano, inda kuma kungiyar ta karbi samfarerear shinkafa Tan 40 daga manoma don inganta tallan su yayin da kungiyoyin mata 40 suka amfana da injInan sarrafa shinkafa da sarrafa gyada a cibiyar wucin gadi da aka tanadar musu.
Solacebase ta ruwaito cewa an gudanar da taron na kwanaki biyu ne a karshen mako.
Saudat Mohammad, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar wadda uwar marayu ce mai ‘ya’ya 5 ta nuna godiyarta ga kungiyar ta WOFAN bisa tallafin da ta bayyana shi a matsayin na jin kai da aka yi musu.

Ba zan manta da wannan rana ba a rayuwata kuma za mu ci gaba da yi wa Hajiya Salamatu Garba addua, An ba mu Naira dubu goma kowannenmu, babbar laimar kasuwanci da mudu 10 na shinkafa da gyada.
A nasa bangaren, dagacin Yan Kusa, da ke karamar hukumar Kumbotso, Malam Danlami yan Kusa, ya ce, guda daga cikin manyan kalubalen da ke haifar da rashin ci gaban tattalin arzikin yankin shi ne rashin tallafi ga kananan sanaoi, musamman na mata.
Haka kuma ya ce, WOFAN ta raba kayan abinci da wasu kayan aiki ga matanmu da matasanmu, wanda hakan zai taimaka matuka wajen taimaka wa harkokin kasuwancinsu.
Haka nan, a yankin Gaida, kusan masu cin gajiyar 240 da aka zabo wadanda mata ne da ƙungiyoyin matasa an tallafa musu da injin gyaran shinkafa da guda biyu wanda kudinsa ya kai Naira 650,000 kowannensu da kuma buhunan samfarerar shinkafa da gyada don haɓaka kasuwancin su.
Shugabar kungiyar a jawabinta yayin shirin ta ce, WOFAN ta kuma fara wayar da kan mutane marasa galihu 100 a kokarin inganta rayuwarsu.
Wadda ta kafa kungiyar ta mata manoma ta WOFAN, Hajiya Salamatu Garba kwanan nan ta lashe gasar Value4her ta masu tallafa wa masu gudanar da kananan sanaoin dogaro da kai ta bana mai taken WAYA2021 a taron 2021 Africa Green Revolution Forum AGRF da aka gudanar a kasar Kenya, inda sama da manoma 2,500 suka fafata daga kasashen Afirka 21.













































