Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa FRSC shiyyar jihar Kwara, ta tabbatar da mutuwar mutane 11 sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da su.
Shugaban hukumar shiyyar jihar Jonathan Owoade, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a Ilorin babban birnin jihar, yana mai cewa hatsarin ya afku ne a kan titin Jebba zuwa Bode.
Haka kuma ya kara da ce, hatsarin ya ritsa ne da wata motar gida kirar Toyota Corolla mai lamba AAA 250 CB da wata motar haya kirar Toyota Hiace mai dauke da lamba LAP 179 XA.
Kwamandan ya ce, hatsarin ya ritsa da mutane 26 inda 15 suka jikkata yayin da 11 suka rasa rayukansu.
Jonathan Owoade, ya kara da cewa, sun samu kiran gaggawa ne inda aka sanar da su faruwar hatsarin da misalin karfe 4:00 na yammacin jiya Lahadi a kauyen Onipako sakamakon aron hannu da gdun wuce sa a.
Ya ce, “Ba ma fatan sake ganin irin wannan mummunan hatsari, Ina rokokon direbobi musamman na motocin haya da su kasance masu hakuri yayin da suke tuki domin kauce wa afkuwar hadura”.
“Rai guda daya ne, babu wani mutum da yake da kari.” In ji kwamandan.
Haka kuma ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin gwamnatin tarayya da ke Jebba da kuma Emmanuel Hospital, yayin da aka mika gawarwakin wadanda suka mutu asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin.













































