Malaman jami’o’in da ke yajin aiki a karkashin kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU na shirin ganawa da wakilan gwamnatin tarayya a ranar Talata kan matakin da ta dauka na tsawon lokaci suna gudanar da yajin aiki.
Shugaban Kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, a ranar Litinin, lokacin da yake magana ta cikin shirin harkokin siyasa a yau na tashar Channel, ya ce ana sa ran yayin taron za a tattauna daya daga cikin batutuwa bakwai da ASUU ke tada jijiyar wuya a kai.
“Wannan shi ne batun da muke fatan sake tattaunawa,” in ji Osodeke, “sake tattaunawa akan yarjejeniyar Shekarar 2009.
“Ba batun albashi kawai ba ne. Batun yana da alaka da tsarin cin gashin Kan Jami’o’i da tsarin biyan kudade da sauran batutuwa; da kuma yadda ake ba da tallafin jami’o’i.
“Gwamnati ta rage batutuwan zuwa ga batun albashi kawai. Amma da a ce sun duba duk yarjejeniyar kuma sun aiwatar da ita, ba za mu yi maganar samar da kudade ba.”

Farfesa Osodeke ya yi albishir da cewa matukar taron na ranar Talata ya yi kyau, za a iya janye yajin aikin. “Muna shirye mu sanya hannu,” in ji shi.













































