Asibitin Aminu Kano zai fara dashen ɓargo

AKTH NEW
AKTH NEW

Asibitin koyarwa na Aminu Kano, AKTH, da ke Kano, a yau Litinin ya ƙaddamar da wani sabon sashin kula da cututtukan jini kuma hakan ya nuna cewa za a fara dashen ɓargo a cibiyar.

AKTH zai kasance asibitin koyarwa na biyu a Nijeriya da zai riƙa yin dashen ɓargo a kasar.

Babban Daraktan Asibitin, Farfesa Abba Sheshe ne ya bayyana haka a wurin kaddamar da cibiyar a hukumance, wanda wani Injiniya Umar lbrahim ya bada ita a matsayin gudunmawa.

Ya bayyana cewa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas ne kadai ya yi nasarar dashen ɓargo a Najeriya.

Ya kuma jaddada cewa kayan aikin da za a sanya a cibiyar za su sanya a samu nasarar dashen ɓargo a asibitin.

Ya yabawa mai bayarwa lbrahim, kuma yayi addu’ar Allah ya saka masa da alkhairi.

Da yake jawabi a madadin mai bayar da tallafin, Farfesa Mahmoud Daneji, ya ce an yi hakan ne domin tunawa da marigayiya mahaifiyarsa.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar ayyukan da aka gudanar a unguwar, da su yi wa mahaifiyar wanda ya bada gudunmawar addu’a, da shi kansa da kuma dukkan iyalanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here