Hukumar zaben ƙasar Kenya ta sanar da William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Kenya da kashi 50.49 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
Hukumar zaɓen ta sanar da sakamakon zaben ne a ranar Litinin da yamma.
An gudanar da zaɓen ne a ranar Talatar da ta wuce 9 ga watan Agustan 2022.
A yayin da yake jawabi bayan sanar da nasararsa, William Ruto ya ce “Yammaci ne mai matuƙar daɗi…
Ratar da ke tsakaninsa da abokin fafatawarsa Raila Odinga ba shi da yawa, inda shi Odingan ya samu kashi 50.4 na yawan uri’un.
An jinkirta sanar da sakamakon saboda zarge-zargen maguɗi da aka dinga yi wa ɓangaren Odinga.
Huɗu daga cikin mambobin hukumar zaɓen bakwai sun ƙi su amince da a fitar da sanarwar sakamakon, suna cewa an yi maguɗi.
“Ba za mu yarda da sakamakon zaɓen ba saboda irin maguɗin da aka tafka a zagaye na ƙarshe na zaɓen,” in ji Juliana Cherera, mataimakiyar shugaban hukumar zaɓen.
“Za mu bayar da cikakken bayani… sannan muna sake roƙon al’ummar Kenya da su kwantar da hankalinsu. Akwai damar zuwa kotu kuma shari’ar za ta yi abin da ya dace,” in ji ta.













































