Kano: Kansiloli sun dakatar da shugaban ƙaramar hukuma na tsawon watanni

Kano Map 1
Kano Map 1

Kansilolin ƙaramar hukumar Bichi ta jihar Kano, sun dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Farfesa Yusuf Muhammad Sabo na tsawon watanni uku.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Bichi, shugaban Kansilolin karamar hukumar, Muhammad Rabo Umar Tinki, Kansila mai wakiltar mazaɓar Kwamarawa, ya ce dakatarwar ta zama wajibi bisa la’akari da rashin cancantar shugaban ƙaramar hukumar.

A cewarsa shugaban ƙaramar hukumar ya gaza gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya tanada a karamar hukumar.

Tinki ya ƙara da cewa Kansilolin sun sha matsin lamba kuma sun kasa kare kansu daga mazaɓunsu saboda shugaban ba ya gudanar da ayyukansa na cigaban ƙaramar hukumar bisa tsari.

Haka kuma, ya ƙara da cewa dakatarwar ta biyo bayan shawarar da majalisar Kansilolin ta yanke bayan kammala tattaunawa a taron da suka yi kwanan nan.

“Yanzu zai yi aiki da dakatarwar kuma kwamitin da aka kafa don bincikar lamarin zai gabatar da rahoto da shawarwarin sa a kan lokaci,” in ji shi.

Solacebase ta tuntubi shugaban karamar hukumar ta Bichi Farfesa Yusuf Muhammad Sabo amma wayarsa a kashe kuma bai amsa saƙon da muka aike masa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here