Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Manir Muhammad Dan’iya, dake matsayin kwamishinan kananan hukumomi da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar, Mallam Saidu Umar, sun ajiye mukamansu, domin neman takara a babban zaben shekarar 2023.
A wata sanarwa da mashawarci na musamman ga Gwamna Aminu Tambuwal, kan harkokin yada labarai, Muhammad Bello, yace karin wasu kwamishinoni 10 suma sun ajiye mukamansu domin tsayawa takarkarun da suke da muradi.
A cewar sanarwar Kwamishinonin sune Kwamishinan Kudi Abdussamad Dasuki, da Kwamishinan Muhalli Sagir Bafarawa sai Kwamishinan Matasa da Wasanni, Bashir Gorau da kuma Kwamishinan Kasa, da gidaje, Aminu Bala.
Sauran sun hadar da: Kwamishinan Kasuwanci, dana ayyuka, dana Albarkatun Ruwa, sai na Addini dana Albarkatun Kasa, da suka hadar da Bashir Gidado da Salihu Maidaji da Shuaibu Gwanda-Gobir da Abubakar Maikudi sai Abdullahi Maigwandu da kuma Kanal Garba Moyi mai ritaya ko wannen su.
Kazalika sanarwar ta kara da cewa Shugaban Ma’aikatan Gwamnan jihar, Mukhtar Magori, shima ya ajiye mukamansa domin tsayawa takarar.













































