Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), ta tabbatar da mutuwar mutane 16 tare da lalata gidaje 3,936 sakamakon ambaliyar ruwa.
Ya kuma ce ambaliya ta kuma mamaye kadada 2,744 na gonaki biyo bayan mamakon ruwan sama tun da aka fara daminar shekarar 2024.
Sakataren zartarwa na hukumar, Dakta Haruna Mariga, wanda ya bayyana hakan a Dutse ranar Laraba, ya ce bala’in ya shafi kananan hukumomi 10 na jihar.
Mairiga ya ce mutanen sun mutu ne sakamakon rugujewar gine-gine, nutsewa da kwalekwale.
Ya ce bala’in ya yi sanadin mutuwar mutane 16 tare da mutane 3,936 da suka rasa matsugunansu yayin da hekta 2,744 na gonaki suka nutse,” in ji shi.
Ya kara da cewa lamarin na iya kara kamari saboda yawan ruwan sama da ake sa ran za’a yi.
Mairiga ya ce hukumar ta samar da matsuguni na wucin gadi tare da raba kayan agaji ga ‘yan gudun hijirar domin rage musu radadi.
Ya jera kayayyakin da suka hada da shinkafa, masara, gyadar masara, barguna, taliya, da tabarmi. (NAN)