Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin bada tallafin karatu a ketare na tsawon shekaru 5

Morufu Tunji Alausa 678x430

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya sanar da dakatar da shirin yarjejeniyar ilimi tsakanin kasashe biyu (BEA) na tsawon shekaru biyar don inganta haɓaka ɗalibai, ba da fifiko ga walwala, da kuma ƙarfafa tsarin ilimin Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Mrs Boriowo Folasade ya fitar a Abuja ranar Asabar.

Ministan ya yi wannan magana ne bayan wani cikakken nazari na shirye-shiryen ilimi da ake samu a kasashen ketare.

Alausa ya ce shawarar ta biyo bayan tantancewar da aka yi wanda ya nuna cewa duk kwasa-kwasan da ake bayarwa a kasashen waje ta tsarin na BEA a halin yanzu ana samun su a Najeriya, kuma a lokuta da dama, an inganta su a cikin cibiyoyin ilimin Najeriyar.

Karin karatu: Gwamnatin tarayya ta soke shirin tallafin karatu na kasashen waje

Ya bayyana cewa, duk da cewa dakatarwar tana karfafa wa ‘yan Najeriya kwarin gwiwar yin karatu a cikin gida, amma hakan bai hana iyaye daukar nauyin ‘ya’yansu karatu a ketare ba.

Ya kara da cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya za ta yi maraba da kasashen da ake yin yarjejeniyar ta BEA da ke ba da cikakken kudin tallafin karatu ga ‘yan Najeriya.

Alausa ya kuma jaddada cewa dakatarwar ba za ta shafi wasu tsare-tsare na bayar da tallafin karatu na gwamnati ba kamar kyautar tallafin karatu a Najeriya ga dalibai a jami’o’in gwamnati da kwalejin kimiyya da fasaha, da lambar yabo ta ilimi ga daliban da ke karatun digiri, da bayar da tallafin karatu na shugaban kasa ga tsofaffin ‘yan bautar kasa na NYSC.

Ya kuma yi karin haske kan inganta tsarin bayar da lamuni na daliban Najeriya, wanda a yanzu haka ke bayar da tallafin kudi ga daliban da suka yi rajista a manyan makarantu na cikin gida.

Alausa ya ba da tabbacin cewa duk wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu na BEA a halin yanzu za su ci gaba da samun cikakken tallafin gwamnati har sai sun kammala karatunsu sun dawo Najeriya. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here