Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta tsawaita yajin aikin gargadi har zuwa watanni biyu.
An dauki matakin tsawaita yajin aikin ne a taron majalisar zartarwar Kungiyar na kasa da aka gudanar a Abuja a daren jiya.
Duk da cewa kungiyar ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da sakamakon taron, wani dan kungiyar da ya yi magana da manema labarai da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce watanni biyun ne za su bai wa gwamnatin tarayya damar biya musu bukatunsu.
Majiyar ta ce sakamakon taron, ana shirin fitar da shi cikin wata sanarwa ga manema labarai nan ba da jimawa ba.