Kungiyar ASUU ta bada tallafin karatu ga wasu hazikan dalibai biyu na Jami’ar Bayero dake Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an bawa daliban tallafin ne karkashin shirin ASUU na bayar da tallafin karatu na shekara-shekara.
Karanra wannan:Gwamnatin tarayya ta cire Jami’o’I daga tsarin biyan albashi na IPPIS
A wata sanarwar hadin gwiwa da Kwamared Sagir Saleh da Kwamared Kabiru Haruna Isa, suka sanyawa hannu.
Tace an bayar da tallafin ga wadanda suka ci gajiyar shirin a wani taro da aka gudanar a sakatariyar kungiyar da ke tsohuwar jami’ar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce shirin na da nufin tallafawa ilimin hazikan dalibai marasa galihu.